Accessibility links

Breaking News

Mayarwa Cambodia Kayayyakin Tarihinta Da Aka Sace


Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken

 A ziyarar da ya kai kasar Cambodia kwanan nan, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya inganta alakar da ke tsakanin kasashen biyu da jama'a tsakanin Amurka da Cambodia. Ya kuma  jaddada cewa, Amurka ta himmatu wajen kiyaye al'adun gargajiya da dukiyoyin jama'a.

Amurka ta yi imanin cewa ya kamata a mayar da kayayyakin tarihi na al'adun gargajiya da aka sace zuwa kasashensu na asali. Kwanan nan, mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka kan harkokin ilimi da al'adu Lee Satterfield ta gana da jakadan Cambodia a Amurka Keo Chhea a birnin New York domin bikin mayar da kayayyakin tarihi na Cambodia guda 30 masu mahimmancin al'adu da addini.

A lokacin rikice-rikicen al’umma na Kambodiya a ƙarshen karni na 20, an sace mutum-mutumi da sauran kayyayakin tarihi daga kambodyia kuma an sayar da su a kasuwannin fasaha na duniya ta shiryayyiyar hanyar sata.

Tawagar masu aikata laifuka na yankin sun sace mutum-mutumin tare da kai su kan iyakar Cambodiya da Thailand, inda dillalai ke kai su gawasu dillalan a Thailand. Waɗannan dillalan za su sayar da kayan tarihi ga abokan cinikin gida ko na ƙasashen waje, waɗanda za su riƙe ragowar ko sayar da su a kasuwar fasaha ta duniya.

Dillalan kayan tarihi zai siyar da guda 30 ga wanda ya mallaka na yanzu da takardun bogi da nufin boye gaskiyar cewa an wawashe kayan tarihnin ne. Mai tattara kayan yana sallama kayan tarihin dan radin kan shi, a cewar Ofishin Lauyan Amurka na Gundumar Kudancin New York.

A karni na 10 "Skanda on a Peacock" da wasu muhimman mutum-mutumi da yawa an sace su daga haikalin Prasat Krachap a 1997 daga wani tsohon mamba na Khmer Rouge.

"Skanda on a Peacock" yana kwatanta abun bautar Hindu na yaki, Skanda, zaune kan dawisu. Jiki da jela na dawisun an yi musu ado da ƙirƙira zane-zane. Masana al'adun Khmer sun yi imanin cewa fuskar Skanda a kan mutum-mutumi na iya zama kamanni na dan gidan sarauta.

A ziyarar da ya kai kasar Cambodia kwanan nan, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya inganta alakar da ke tsakanin kasashen biyu da jama'a tsakanin Amurka da Kambodia. Ya kuma jaddada cewa, Amurka ta himmatu wajen kiyaye al'adun gargajiya da dukiyoyin jama'a a Kambodia da ma duniya baki daya.

"Daya daga cikin abubuwan da nake alfahari da su," in ji Sakatare Blinken, "shi ne muna maido da kayayyakin tarihi na al'adun gargajiya da aka sace daga Cambodia kuma muna tabbatar da cewa an dawo da su, wani abu da nake ji da shi sosai."

XS
SM
MD
LG