Sama da shekaru 40 kenan da Amurka ta kirkiri shirin tallafawa kasashen da take kawance da su kan dabarun yaki da ta’addanci. A wani taron manema labarai da aka gudanar, Julie Cabus, na’ibin mataimakin sakataren Amurka kuma mataimakiyar darekta mai ba da horo a ma’aikatar tsaro na diflomasiyya, ta sheda cewa, tun daga lokacin da aka kirkiri shirin, ATA ya horara da sama da dalibai dalibai 160,000 dabarun yaki da ta’addanci a kasashe mabanbanta 150:
“A bara kawai, shirin ATA, ya horar da kusan dalubai 5,000, kimanin dalibai 4,700, akalla a kasashe mabanbanta 47.
Tun bayan kirkirar shirin, ATA ya zama wata kafar da ta bayyana hadin kai na hakika a tsakanin ma’aikatar tsaron Amurka da kasashen duniya akan shawo kan kalubalen da ya addabi duniya na ta’addanci da kuma yaki da ta’addanci.
Shirin ATA, shiri ne da alhakin nasararsa ya rataya a wuyan sashen yaki da ta’addanci da ayyukan diflomasiyya na ma’aikatar tsaron Amurka.
Gregory LoGerfo, shi ne mataimakin jami’i mai lura da al’amuran mu’amala da yankunan kasashen wajen a cibiyar yaki da ta’addanci, ya kuma jaddada irin dangantakar hadin kan da ke tsakanin Amurka da kasashe inda suka samu horasawar ATA.
“Muna kulawa da bukatun abokan hadin gwiwarmu, abubuwan da suke damunsu na musamman domin suna fuskantar matsaloli mabanbanta a kasashensu da kuma yankunan su… Muna kokarin kwatanta samun daidaito a bangaren hadin gwiwar da muke kullawa domin baki daya maradun mu shine fuskantar kalubalolin tsaron fararen hula.”
Na’ibar, mataimakiyar Sakatare Cabus ta kuma sheda cewa yaki da ta’addanci yana bukatar karfi kana, yana bukatar amfani da hankali sannan kuma masu ba da horon shirin na ATA suna bukatar daliban su kasance masu hazaka.
“Suna samar da yanayin da ke bai wa mahallarta taron damar gwada darussan da ake koya musu na dabarun horon, da dabarun yanke shawara da kuma musayar ra’ayoyi da abokan hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da abokansu a fadin duniya”.
Bayan nan, Cabus ta yi tsokaci a game da wani muhimmin fannin shirin na ATA wanda yake jaddada mahimmancin tabbatar da ingantacen tsarin