Shirin 'Global Criminal Justice Rewards Program' na Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka zai ta ba da har dala miliyan 5 ga mutanen da suka ba da bayanan da zai kai ga kamawa, canja wuri, ko yanke hukunci kan 'yan Rwanda Charles Sikubwabo ko Ryandikayo.
A lokacin kisan kare dangi na Rwanda, Sikubwabo shi ne magajin garin Gishyita. Ana zargin Sikubwabo da haddasa kisan kiyashi a cocin Mubuga da sauran wurare, tare da hada gwiwa da wasu don kawo 'yan Jandarma na kasa, 'yan sandan jama'a, Interhamwe, da fararen hula dauke da makamai zuwa yankin tare da ba su umarnin kashe 'yan Tutsi.
Ana kuma zargin Ryandikayo da haddasa kisan kiyashi a cocin Mubuga da kuma taimakawa wajen jagorantar 'yan Jandarma, 'yan sandan jama'a, 'yan bindigan Interhamwe, da fararen hula dauke da makamai domin kai hari cocin tare da kashe wadanda suke ciki. Ana kuma zargin Ryandikayo da hannu a kashe-kashe na kai tsaye.
Charles Sikubwabo da Ryandikayo dai ana neman su ne karkashin tsari na kasa da kasa na “Residual Mechanism for Criminal Tribunals” saboda laifukan da ake tuhumar su da su, in ji Beth Van Schaack, jakadana a kungiyar Large ta Global Criminal Justice.
“Waɗannan mutane biyu ne da ake zargi da hannu a kisan kiyashin da aka yi a Rwanda a shekara ta 1994. Don haka, har yanzu ana bayar da tukwici ga bayanan da za su kai ga kama su.”
Tukwicin da za a bayar na kama Charles Sikubwabo da Ryandikayo ya kai dala miliyan 5 kowannensu, amma akwai wasu ka’idoji, in ji Ambassador Van Schaack.
“Saboda haka, na ɗaya, mutum ba zai kawo su a mace ba. Dole ne a kai su gidan yari. Na biyu, bayanin ya zama daidai, kuma dole ne ya kai ga kama su. Don haka wannan muhimmin bambanci ne. Kuma ba za a iya bayar da tukwici ba idan ƙoƙarin kama su ya ci tura. Kuma a ƙarshe, ba za mu iya ba da kafin alkalami ba.”
Idan wani yana da bayani game da Charles Sikubwabo ko Ryandikayo, da fatan za a tuntuɓi Shirin Ba da Ladan Adalci na Duniya ta hanyar saƙon rubutu, SMS, ko WhatsApp akan: +1-202-975-5468 ko ta imel a: GCJRP@state.gov. Hakanan zaka iya kawo bayanai zuwa Ofishin Jakadancin Amurka mafi kusa ko kowane jami'in Gwamnatin Amurka. Za a sirrinta duk bayanan da aka samu.
Wannan sharhi ne da ke nuna ra'ayin Gwamnatin Amurka.