Accessibility links

Breaking News

Amurka Na Goyon Bayan Gwamnatocin Da Ke Bin Tafarkin Dimokradiyya A Afirka


Shugaban Amurka, Joe Biden
Shugaban Amurka, Joe Biden

 "Afrika ta fi karfin ‘yan waje da ke  ƙoƙarin mallake nahiyar. Kuma Afirka ta fi karfin masu mulkin kama karya da ke siyar da bindigogi masu arha, tura sojojin haya kamar kungiyar Wagner, ko hana hatsi ga masu fama da yunwa a duniya."

"Gwamnatin Biden ta yi amannar cewa ana kafa tarihi a nahiyar Afirka. Kuma muna son ci gaba tare, ta hanyar samun bunkasuwa tare da hadin gwiwa da mutunta juna,” in ji sakataren tsaron kasar Lloyd Austin yayin ziyararsa ta farko zuwa Afirka a matsayin sakatare.

Da yake magana a Angola bayan ya ziyarci Djibouti da Kenya, Sakatare Austin ya mayar da hankali kan kawancen tsaro don tunkarar barazanar karni 21 cikin gaggawa:

“Wadannan barazanar sun haɗa da tsattsauran ra'ayi, satar fasaha, da bala'o'in yanayi - galibi suna ƙara yin muni ta hanyar rashin shugabanci mai karfi, da cibiyoyi masu cin zarafi, da kuma talauci. Don haka mun kuduri aniyar yin aiki tare da abokan huldarmu na Afirka don bunkasa karfin da suke bukata don kiyaye mutanensu. ... Wannan ya haɗa da ilimin soja mai zurfi, yaƙi da ta'addanci, dabaru da dai sauransu da dama. "

"Ayyukanmu da muke yi tare, na goyon bayan sha'awarmu ta tabbatar da tsaro, mai juriya, da bude kofar Afirka, bisa dokoki da ka'idoji da ke ba kowa damar ci gaba," in ji Sakataren Tsaro Austin.

"Afrika ta fi karfin ‘yan waje da ke ƙoƙarin mallake nahiyar. Kuma Afirka ta fi karfin masu mulkin kama karya da ke siyar da bindigogi masu arha, tura sojojin haya kamar kungiyar Wagner, ko hana hatsi ga masu fama da yunwa a duniya."

Afirka," in ji shi, "na buƙatar shugabannin farar hula waɗanda suka ci gaba da yin imani da ƴan ƙasarsu kuma suna sauraron ra’ayoyinsu."

A dai dai lokacin da wasu kasashen Afirka da dama suka fuskanci daukar matakin juyin mulkin soji a baya-bayan nan, Sakatare Austin ya jaddada muhimmancin ajiye dakarun kasa karkashin mulkin farar hula

“Idan sojoji suka yi watsi da zabin jama’a, suka kuma fifita burinsu a kan doka, tsaro kan tabarbare – kuma dimokradiyya ta mutu. … Afirka na buƙatar sojojin da ke yi wa ƴan ƙasarsu hidima - ba akasin haka ba.

Amurka, in ji Sakatare Austin, “za ta ci gaba da saka hannun jari a cikin kwararrun sojojin da farar hula ke jagoranta. Za mu yi aiki tare don zurfafa ka'idoji don kawar da gwamnatocin dimokradiyya. Kuma za mu kasance masu gaskiya tare da abokan aikinmu lokacin da cibiyoyin tsaron su suka gaza cika waɗannan ka'idoji na duniya."

Tsarin dimokradiyya, in ji Sakatare Austin, ba abu ne mai sauki ba kuma ba cikakke ba ne. "Amma ita ce hanya mafi kyau kuma mara tsawo wajen samun dawwamammen zaman lafiya da wadata. Hanya ce da miliyoyin maza da mata a fadin wannan nahiya suka zaba cikin 'yanci. Kuma Amurka," in ji shi, "tana alfahari da tsayawa tare da duk wadanda ke neman gwamnatocin 'yanci, bude kofa ga tsarin dimokradiyya a Afirka."

XS
SM
MD
LG