Accessibility links

Breaking News

Ya Kamata Maduro Ya Koma Teburin Tattaunawa Da ‘Yan adawa - Amurka


Sakatare Antony Blinken
Sakatare Antony Blinken

"Gamayyar ‘yan adawar ta Unitary Platform a shirye take ta gana da su... Kuma idan suka sami ci gaba a wannan fanni, Amurka za ta yi maraba da shi."

Gwamnatin Maduro ta Venezuela ta kauracewa sabon zagayen tattaunawa da gamayyar 'yan adawa wanda aka yi tsakanin ranakun zuwa 17-20 na Oktoba a Mexico. Wannan tattaunawa wacce aka faro a hukumance a ranar 3 ga Satumba, ta dan ba da kwarin gwiwar samun haske ga maido da tsarin dimokradiyya a kasar ta Venezuela.

Maduro ya ki aike da tawaga zuwa zagaye na baya-bayan nan na tattaunawar bayan da aka tasa keyar wani makusancinsa kuma mai haramtaccen kudi, Alex Saab, zuwa Amurka inda aka tuhume shi a shekarar 2019 bisa laifin karkatar da kudade da kuma karya dokar hana cin hanci da rashawa ta Amurka ta (FCPA).

Da aka tambaye shi a wani taron manema labarai game da shawarar da Maduro ya yanke na ficewa daga tattaunawar, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kwatanta lamarin a matsayin "abu mai matukar ban takaici."

"Wannan ya nuna cewa Mr Maduro ya fi fifita bukatunsa na kansa fiye da na al’umar Venezuela, wannan babban abin takaici ne.” in ji Mista Blinken.

Ya kuma yi nuni da tuhumar aikata laifuka da ake yi wa Alex Saab wanda y ace an kwashe tsawon lokaci ana yin ta, “kuma hakan, wani abu ne da ke nuni da cewa bangaren shari’ar Amurka na cin gashin kansa, ta hanyar tsame hannunsa a duk wani da ya shafi siyasa,” kamar batun tattaunawa tsakanin gwamnatin Maduro da bangaren gamayyar ‘yan adawa.

Da aka tambaye shi a wani taron manema labarai na daban game da Citgo-6 da kuma kauracewa Maduro kan tattaunawar Venezuelan, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price ya ce Maduro ya dauki shugabannin shida a matsayin "yan siyasa," wadanda aka gallazawa ta hanyar tsare su ba bisa ka’ida ba.” Price ya yi kira ga Maduro da ya sake su "cikin gaggawa kuma ba tare da wani sharadi ba."

Mista Price ya bayyana cewa, "Amurka na goyan bayan shawarwarin da Venezuelan ke jagoranta tsakanin 'yan adawar Unity Platform da gwamnatin Maduro… kuma muna ci gaba da fatan cewa hakan zai kai ga maido da mulkin dimokradiyya cikin lumana wanda mutanen Venezuela suke so kuma suka cancanci su samu.”

A wata ziyarar da ya kai a baya-bayan nan, Mataimakin Sakataren Harkokin Yammacin Duniya Brian Nichols ya ce, "Idan gwamnatin Maduro ta kasance da gaske kan samar da makoma mai kyau ga al'ummarta, da magance matsalolin jin kai da ke fama, gwamnatin Maduro na iya nuna hakan ta hanyar komawa kan teburin sasantawa.

Gamayyar ‘yan adawar ta Unitary Platform a shirye take ta gana da su... Kuma idan suka sami ci gaba a wannan fanni, Amurka za ta yi maraba da shi."

XS
SM
MD
LG