Accessibility links

Breaking News

Ya Zama Wajibi Gwamnatin Sudan ta Kudu Ta Sauya Salon Tafiya


Thomas-Greenfield, Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya
Thomas-Greenfield, Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya

Amurka ta sake yin kira ga gwamnatin Sudan ta Kudu, da ta yi zabin da ya dace. Shekaru 12 bayan samun ‘yancin kai, lokaci ya wuce da gwamnatin rikon kwarya za ta bude sabon babi.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield ta bayyana takaicin cewa cikin watanni shida da suka gabata a Sudan ta Kudu “sauyin da aka samu bai taka kara ya karya ba.”

Amurka ta yarda cewa “rashin mayar da hankali na ‘yan siyasa” shi ne tushen wannan rashin amincewa, in ji Ambasada Thomas Green-Field. Hakika, ba’a iya warware irin wadannan batutuwan da aka gano watannin shida da suka wuce ba.

“Tambayoyin na asali game da wa za su kada kuri’a, ta yaya za su kada kuri’a, da matakan gwamnati da za su zaba, duk ba’a amsa su ba. Yayin da gwamnatin rikon kwarya ta yi aiki dan kadan wajen shirya zabuka, samar da karin kudade ga wadannan zabuka na aike wa da sako mara kyau.”

Gwamnatin rikon kwarya ta Sudan ta Kudu na samun kudaden shigarta daga albarkatun man fetur domin gudanar da ayyukan gwamnati, in ji Ambsada Thomas-Greenfiled:

“Al’ummar Sudan ta Kudu na da ‘yancin sanin yadda ake kashe kudaden man kasarsu da kuma yadda suke amfana da kudaden man kasarsu. Don haka, dole ne gwamnati rikon kwarya ta fara amfani da kudaden shiga na jama’a a fili don amfanin jam’a da suka dace.”

Ambasada Thomas Greenfiled ta ce, “bugu da kari, muna cikin damuwa da yawan tashin hankali, aikata laifuka da take hakkin dan adam a Sudan ta Kudu.”

“Mun sanya Gordon Koang Biel da Gatluak Nyang Hoth da Joseph Mantiel Wajang, a matsayin wadanda ke da alhakin yi wa mata da ‘yan mata fyade da kuma sauran laifukan cin zarafin bil adama a lokacin harin da ‘yan bindiga suka kai a gundumar Leer ta jihar Unity. Wadannan kungiyoyi masu dauke da makamai sun yi amfani da bautar wa ta hanyar jima’i, da suka hada da fyade na kungiyoyi, na mata da ‘yan mata da aka sace a matsayin karfafawa da lada ga mayakan. Wannan zalunci ne mara misaltuwa. Don haka, mun yi kira ga shugaban Kiir da ya cika alkawarin da ya dauka na hukunta wadanda suka aikata wadannan ayyukan da ba’a taba tsammani ba.”

Gwamnatin rikon kwaryar ta Sudan ta Kudu tana da zabuka da dama: ko ta cimma alkawarun da aka kulla a yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2018 da ta wajaba ta gudanar da zabuka na gaskiya ba tare da magudi ba a cikin watanni 12; ko ta yi amfani da dimbin kudaden shigarta na jama’a don tabbatar da cewa mutanen Sudan sun samu isasshen abinci. Sannan ko a hukunta masu take hakkin dan adam.

Amurka ta sake yin kira ga gwamnatin Sudan ta Kudu, da ta yi zabin da ya dace. Shekaru 12 bayan samun ‘yancin kai, lokaci ya wuce da gwamnatin rikon kwarya za ta bude sabon babi.

XS
SM
MD
LG