Na dawo fadar shugaban kasa da kwarin gwiwa da kuma kwarin gwiwar cewa mun shiga farkon wani sabon babi na samun nasara a kasar nan," in ji Shugaba Donald Trump a jawabinsa na farko ga al'ummar kasar a matsayin shugaban kasa na 47.
“Ba za a ƙara hana ’yancinmu da makomar al’ummarmu ba. Kuma nan take za mu maido da mutunci, cancanta, da amincin gwamnatin Amurka."
"Fadi tashin da muka yi wajen kwato jamhuriyarmu ba abu ne mai sauki ba," in ji Shugaba Trump:
“Bayan ’yan watanni da suka shige, a wani kyakkyawan fili na Pennsylvania, wani harsashi da ya bullo ya tsaga kunnena. Amma na ji a lokacin kuma na gaskanta har yanzu cewa raina ya sami ceto saboda wani muhimmin dalili. Allah ne ya kubutar da ni don in sake maido da martabar Amurka.”
"Wannan shi ya sa kowace rana.... za mu dukufa cikin sauri don maido da kyakkyawan fata, ci gaba da tsaroda zaman lafiya ga kowanne dan kasa ba tare da yin la’akkari da jinsi, ko addini ko launin fata ko wata dangantaka ba.”
Shugaba Trump ya ba da sanarwar cewa zai fara wa'adinsa tare da sanya hannu kan wasu jerin umarni na gashin kansa don "fara dawo da martabar Amurka da juyin hali mai ma’ana."
Da farko, Shugaba Trump ya ayyana dokar ta-baci ta kasa a iyakar kudancin kasar. Wadda ta fara aikin mayar da miliyoyin baƙi masu laifi zuwa wuraren da suka fito.
Shugaba Trump ya ayyana kungiyoyin masu safarar miyagun kwayoyi a matsayin kungiyoyin ta'addanci na kasashen waje.
A wani yunƙuri na sauƙaƙan hauhawar farashin kayayyaki, shugaba Trump ya ayyana dokar ta-baci a fannin samar da makamashi domin a gaggauta hako mai da iskar gas a Amurka.
“Amurka za ta sake zama ƙasa mai masana’antu, kuma muna da wani abu da babu wata ƙasa mai ƙere-kere take da shi; muna da man fetur da iskar gas da babu wata kasa take da shi a duniya, kuma za mu yi amfani da shi."
"Kamar yadda muka yi a shekarar 2017, za mu sake karfafa dakarun soji mafi girma da duniya ta taba gani," in ji Shugaba Trump.
“Ba za mu auna nasarar da muka samu ta fuskar yaƙe-yaƙen da muka yi nasara kadai ba, ko yake-yaken da muka dakatar ba – za mu hada har da yakin da ba mu shiga ba.”
Shugaba Trump ya ce "Amurka za ta koma matsayinta na asali, kasa mafi girma da aka fi girmamawa a doron kasa, wanda hakan zai kwadaitar da duniya.”
"Za mu tsaya a matsayin jarumai, za mu rayu cikin alfahari, za mu yi kyakkyawan mafarki, kuma babu abin da zai sha gabanmu saboda mu Amurkawa ne. Lokaci mai zuwa namu ne, kuma yanzu zamaninmu ya fara.”