Irin Ta'asar Da Rasha Ke Aikata wa A Ukraine

Shugaba Joe Biden

Aikin hukumar ya bai wa al’ummomin duniya sanin ainihin abin da ke faruwa na tashin hankalin da fararen hular Ukraine ke fuskanta a kowacce rana

Wajibi ne a mutunta wa tare da kare hakkin dan adam, musamman a lokutan tashin hankali, ya kasance cikin dokokin kasa da kasa. Don hake ne Majalisar Dinkin Duniya ta kafa kwamitin bincike na kasa da kasa mai zaman kansa kan kasar Ukraine, mako guda bayan da Rasha ta mamaye karamar makwabciyarta a ranar 24 ga watan Fabrairu bara.

Aikin hukumar ya bai wa al’ummomin duniya sanin ainihin abin da ke faruwa na tashin hankalin da fararen hular Ukraine ke fuskanta a kowacce rana.

A wani taro na baya bayan nan na Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, wanda Albaniya da Amurka da Burtaniya su ka kaddamar, kwamishononin sun lura cewa, “Shaida ta nuna cewa hukumomin Rasha sun tafka laifuka da dama, wadanda yawancinsu laifukan yaki ne.”

“Sun hada da kashe-kashe da gangan, hare-hare kan fararen hula da tsare mutane ba bisa ka’ida ba da azabtarwa da fyade da cin zarafi da kuma tilasta tasa keyar yara. Sauran cin zarafin sun hada da amfani da makamai masu fashewa a wuraren da jama’a ke da yawa, cikin har da hare-haren wuce gona da iri da kuma hare-hare kan ababen more rayuwa masu alaka da makamashi.”

“Mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ba wai kawai ya sabawa diyaucin Ukraine ba ne; barazana ce kai tsaye ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, kuma tana da munanan abubuwa da su ka shafi hakkin dan adam da na jinkai,” in ji Mai Ba Da Shawara Kan Harkokin Siyasa na Amurka John Kelly.

“Aikin hukumar shine fallasa kisan kiyashi da cin zarafi da aka aikata a yakin Rasha, yana da muhimmanci don tabbatar da an adalci ga dubban wadanda abun ya shafa. Wannan cikakken rahoto na wannan kwamiti ba wai kawai ya samar da fahimtar wannan majalisa ba game da zalunci yakin shugaba Putin, zai kuma taimaka wajen samar da hanyar da za’a bi wajen tabbatar da adalci da kuma duniya mai aminci.”

Rahotan hukumar ba abu bane mai dadin karantawa ba. duk da haka, "yana da muhimmanci duniya ta fahimci abin da ke faruwa," a cewar jakada Kelly.

“Rahotan ya bayar da cikakkiyar kididdigar hare-haren da aka kai a wuraren kiwon lafiya da azabtarwa da cin zarafin jinsi da tilasta tasa keya zuwa wata kasa. Ya kamata ya tilasta mana duka mu yi Allah wadai da halayyar Rasha.”

“Amurka tana matukar goyon bayan hanyoyin tabbatar da adalci da hukunta wadanda su ka yi kisan kiyashi a kan al’ummar Ukraine, kuma za mu ci gaba da ba da goyon baya ga ikon Ukraine don gudanar da bincike da hukunta kisan kiyashi, tare da tallafawa kokarin da ake yi a sauran kotunan kasar da cibiyoyin kasa da kasa,” in ji Jakada Kelley.”

“Ba za mu iya kyale zalunci ba, kuma dole ne mu bayyana kudurinmu na kiyaye dokokin kasa da kasa. Muna sake yin kira ga Shugaba Putin da ya kwao karshen yakin da ya fara ba tare da wata bukata ba da kuma janye dakarun Rasha daga sojojin Rasha daga Ukraine.”