Accessibility links

Breaking News

Sanya Takunkumi Akan Shugabannin Mali Da Suka Aikata Ta’asa


Sojojin hayan Rasha a Mali
Sojojin hayan Rasha a Mali

Ya zuwa lokacin da suka kammala samamen, akalla mutum 500 ne suka mutu. Akwai rahotanni da ke cewa an azabtar da mutane tare an ci zarafin mata akalla 58, ciki har da wadanda aka yi wa fyade.

A karshen watan Maris, dakarun Mali wadanda suka samu goyon bayan sojojin hayan Rasha na Wagner – wata kungiyar masu aikata manyan laifuka da ke yawo kasa da kasa, sun kai wani samamen yaki da ayyukan ta’addanci a Moura, wani kauye da ke yankin Mpoti a tsakiyar Mali.

Ya zuwa lokacin da suka kammala samamen, akalla mutum 500 ne suka mutu. Akwai rahotanni da ke cewa an azabtar da mutane tare an ci zarafin mata akalla 58, ciki har da wadanda aka yi wa fyade.

A karshen watan Mayu, Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta sanya takunkumin biz akan wasu shugabannin Mali biyu wadanda ke da hannu a samamen.

Kanar Moustapha Sangare, shi ne ya jagoranci rundunar dakarun da ke sauka ta lema ta 33 a lokacin, sannna Manjo Lassine Togola yana mukaddashin wata runduna ta musamman mai cin gashin kanta.

Duk mutane biyu, an sanya musu takunkumi karkashin doka ta 7031 © ta Ma’aikatar harkokin wajen Amurka da sauran makamantan laifuka saboda hannu da suke da shi a take hakkin bil Adama.

A wancan lokaci, Ofishin Kula da kadarori ta Ma’aikatar Shari’ar Amurka ko kuma OFAC a takaice, ta sanya Ivan Aleksandrovich Maslov a wani rukuni na 14024 saboda rawar da ya taka a matsayin wakilin Wagner.

Maslov, shi ne Shugaba kuma mai fada a ji a kungiyar Wagner reshen kasar ta Mali

An tuhumi Maslov da jagorantar reshen dakarun na Wagner tare da Yevgeniy Viktorovich Prigzozhin da Valeryevich Utkin, wato babban jagora da kuma asalin wanda ya kafa kungiyar ta Wagner.

Dukkansu biyu, Amurka, Birtaniya, Kungiyar Tarayyar Turai da Canada sun saka musu takunkumi.

A matsayinsa na Shugaba a kungiyar dakarun ta Wagner, Maslov ya yi aiki tare da jami’an gwamnatin Mali wajen aiwatar aikin tura dakaru.

Shi ne da alhakin hada wani zama tsakanin Prigozhin da jami’an gwamnatin wasu kasashen Afirka da dama kuma ya yi aiki wajen wakiltar dakarun na Wagner wajen kwasar arziki na ma’adinai.

“Baitulmalin Amurka ta sanya takunkumi akan jami’I mafi girma da ke wakiltar kungiyar ta Wagner a Mali, ta kuma gano tare da ruguza wasu shirye-shriye da ke goyon bayan ayyukan kungiyar,” In ji Karamin Sakataren Baitulmalin Amurka na sashen yaki da ayyukan ta’addanci Brian Nelson.

Ya kara da cewa, “kasancewar kungiyar ta Wagner a nahiyar Afirka, zai zamanto wani abu da zai wargaza duk wata kasa da ta bari dakarun Wagner suka shiga.”

Sanarwar: Wannan shi ne sharhin Amurka da ke bayyana ra’ayin gwamnatin kasar

XS
SM
MD
LG