Kowace shekara a ranar 11 ga Mayu, Amurka tana bikin ranar 'yancin ɗan adam ta Vietnam, ranar tunawa da mauhimmancin ci gaba da 'yancin walwala da suka haɗa da 'yancin faɗar albarkacin baki, gudanar da taro, cudanya, da yin addini.
Vietnam ta kasance kasa mai iko da jam'iyya daya, Jam'iyyar Kwaminisanci ta Vietnam. A cewar rahoton haƙƙin ‘ɗan adam na baya bayan nan na Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka game da Vietnam, "ba a sami wani gagarumin canje-canje a yanayin 'yancin ‘ɗan adam a Vietnam a cikin shekarar da ta gabata ba."
Dangane da rahotannin kafofin watsa labarai, kungiyoyi masu zaman kansu, da sauran masu sa ido, hukumomin Vietnam har zuwa ranar 31 ga Oktoba sun tsare akalla mutum 187 don fafutukar siyasa ko kare hakkin dan ‘adam, ciki har da masu laifi 162 da 25 a tsare kafin a gurfanar da su gaban kotu.
A cewar kafofin yada labarai da kungiyoyin kare hakkin bil'adama, daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Oktoba, hukumomi sun tsare mutum 25 tare da hukunta wasu 23 da suke gudanar da ayyukan kare hakkin bil'adama da duniya ta amince da su kamar 'yancin fadin albarkacin baki, yin taro cikin lumana, da kuma haduwa. Yawancin waɗannan kame da yanke hukunci na da alaƙa da rubuce-rubucen bayyana ra'ayin mutum na kansa a yanar gizo.
Kundin tsarin mulki da dokar Vietnam sun tanadi ‘yancin fadin albarkacin baki, gami da ‘yan jarida da sauran kafafen yada labarai; duk da haka, a cewar rahoton kare hakkin ‘dan adam, gwamnati ba ta mutunta wadannan hakkoki.
Gwamnati na ci gaba da amfani da faffadan tsare-tsare na tsaron kasa da kuma bata suna a cikin dokar wajen takaita ‘yancin fadin albarkacin baki.
Gwamnatin Vietnam ta takaita kalaman da ke sukar shugabanin gwamnati ko jam'iyya, inganta jam'iyyar siyasa ko dimokuradiyyar jam'iyyu da yawa, ko yin tambayoyi kan manufofi kan batutuwa masu muhimmanci, kamar 'yancin ‘dan adam, 'yancin addini, takaddamar 'yancin kai tare da Jamhuriyar Jama'ar Sin, ko kwace filaye ala tilas.
'Yan jarida masu zaman kansu na ci gaba da fuskantar takunkumi kan 'yancin walwala, da sauran nau'o'in tsangwama, da kuma sauran hare-hare idan sun ba da rahoto kan batutuwa masu muhimmanci, in ji rahoton kare hakkin ‘dan adam.
Gwamnati kuma tana sa ido kan tarurrukan 'yan jarida da sadarwa. Gwamnati na ladabtar da 'yan jarida saboda gazawa wajen tantance kansu, ciki har da ta soke bayanansu.
Gwamnatin Vietnam ta ci gaba da aiwatar da "matsanancin sa ido kan ayyukan addini," in ji sabon rahoton 'Yancin Addini na Duniya. Tabbas, kasar Amurka ta nuna matukar damuwarta a kwanan nan, game da hukunce-hukuncen da ake yi wa tsirarun kabilun Vietnam da masu fafutukar ‘yancin addini. Irin wannan hukunci guda biyar sun faru tun daga watan Janairu.
Kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ya ce, “muna kira ga Vietnam da ta mutunta ‘yancin fadin albarkacin baki, tarayya, da addini ko imani. Ya kara da cewa, "muna sake jaddada kiranmu ga Vietnam da ta saki duk wadanda ake tsare da su ba bisa ka'ida ba."
Wannan sharhi ne da ke nuna ra'ayoyin Gwamnatin Amurka.