Accessibility links

Breaking News

Amurka Ta Ayyana Mambobin ‘Yan ISIS-K  Hudu A Matsayin ‘Yan ta’adda


Shugaban Amurka Joe Biden, ranar 17 ga watan Disamba 2021.
Shugaban Amurka Joe Biden, ranar 17 ga watan Disamba 2021.

"Za mu ci gaba da yin amfani da dukkan karfin ikon Amurka wajen kai hari ga 'yan ta'addan da ke shirya ayyukan kashe fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, da wadanda ke ba da damar, sauƙaƙewa, da kuma ba da kuɗin ayyukansu."

Lardin Khorasan, ko ISIS-K, ƙungiya ce ta ta'addanci da ke aiki a kudanci da tsakiyar Asiya, galibi a Afghanistan, amma kuma tana wasu wurare a Kudancin Asiya. An kafa kungiyar ne shekaru shida da suka gabata ta hannun wasu ‘yan Taliban da ba su amince da shi ba, kungiyar na daukar Taliban a matsayin makiyiya. A cikin shekaru 6 da suka gabata, ISIS-K ta kai munanan hare-hare da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane, musamman a Afghanistan.

Hare-haren sun hada da harin bam na watan Mayun 2021 a wani masallacin Kabul wanda ya kashe akalla masu ibada 12 da suke bikin Eid al-Fitr, da kuma harin bam da aka kai a filin jirgin saman Hamid Karzai na Kabul a watan Agustan 2021 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 170. Yawancin wadanda abin ya shafa fararen hula ne, kuma yawancinsu yara ne, sannan kuma galibi suna kai hari ga addinai marasa rinjaye, ciki har da al'ummomin Shi'a da Sikh.

A karshen watan Nuwamba, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayyana shugabannin ISIS-K uku, tare da daya daga cikin manyan masu taimaka mata a harkokin kudi, a matsayin Musamman Zaɓaɓɓen 'Yan Ta'addan Duniya a ƙarƙashin Dokar Zartarwa 13224, kamar yadda aka gyara.

Sanaullah Ghafari, wanda kuma aka fi sani da Shahab al-Muhajir, shine babban sarkin kungiyar na yanzu. Kungiyar ISIS ce ta nada shi don jagorantar ISIS-K a watan Yuni 2020. Ghafari ne ke da alhakin amincewa da duk ayyukan ISIS-K a duk fadin Afghanistan da kuma shirya kudade don gudanar da ayyuka.

Sultan Aziz Azam, ko Sultan Aziz, shi ne kakakin kungiyar ISIS-K tun lokacin da kungiyar ta fara zuwa Afghanistan.

Maulawi Rajab, wanda kuma aka fi sani da Maulawi Rajab Salahudin, babban jigon kungiyar ISIS-K ne a lardin Kabul na kasar Afghanistan. Yana tsara ayyukan kungiyar kuma yana ba da umarnin kungiyoyin ISIS-K da ke kai hare-hare a Kabul.

An nada Ismatullah Khalozai ne don bayar da tallafin kudi ga kungiyar ISIS-K. Ya kasance mai gudanar da harkokin kudi na kasa-da-kasa na ISIS-K, kuma ya gudanar da ayyuka ga manyan shugabannin ISIS.

“Amurka ta kuduri aniyar yin amfani da dukkanin na’urorinta na yaki da ta’addanci domin tinkarar barazanar da lardin Khorasan na kungiyar IS, wanda aka fi sani da ISIS-K, a matsayin wani bangare na kokarin da muke yi na tabbatar da cewa Afghanistan ba za ta sake zama dandalin ta’addanci na kasa da kasa ba,” in ji sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken a wata rubutacciyar sanarwa.

"Za mu ci gaba da yin amfani da dukkan karfin ikon Amurka wajen kai hari ga 'yan ta'addan da ke shirya ayyukan kashe fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, da wadanda ke ba da damar, sauƙaƙewa, da kuma ba da kuɗin ayyukansu."

XS
SM
MD
LG