Accessibility links

Breaking News

Kassara Kungiyoyin Da Ke Tallafa wa Hizballa A Yankin Kudancin Amurka


Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden

"Za mu ci gaba da kawar da wadanda ke neman yin amfani da tsarin hadahadar kudade na Amurka da na kasa da kasa don samar da kudade da kuma shiga ayyukan ta'addanci."

Amurka ta kai kaikaici manyan jami’an Hizballah da suka kafa cibiya a Kudancin Amurka da Lebanon masu tallafa wa ayyukan ta’addancin Hizballah a Kudancin Amurka.

Tun da farko dai kungiyar Hizballah da ke kasar Lebanon ta kafa wani katafaren ababen more rayuwa na duniya da harkokin kasuwanci da ke bai wa jami'an Hizballah damar yin tafiye-tafiye cikin 'yanci da walwalar kudade.

Ofishin Ma'aikatar Baitulmalin Amurka na Kula da Kaddarori a kasashen Waje, ko OFAC, ya ayyana wasu manyan mutane bakwai da ke aiki da wannan kungiya a matsayin ‘yan ta’adda. Ma’aikatar ta OFAC na aiki ne tare da hukumar da ke sa ido kan sha’anin magunguna.

Amer Mohamed Akil Rada ya dade a kungiyar Hizballah. Yana zaune ne a Lebanon amma ya kwashe sama da shekaru goma a Kudancin Amurka yana aiki a madadin Hizballah. Kusan kashi 80 cikin 100 na abin da yake samu na kasuwancinsa yana zuwa ne ga ayyukan Hizballah. Bugu da ƙari, akwai hanunsa a cikin harin bam din 1994 a cibiyar al'ummar Yahudawa mafi girma a Amurka ta Kudu, wanda ya kashe mutane 85 tare da raunata wasu daruruwa.

Kamar dan uwansa Amer, Samer Akil Rada dan kungiyar Hizballah ne.

An danganta shi da laifukan da suka shafi safarar miyagun kwayoyi da kuma karkatar da kudade a kasashe daban-daban a yankin Amurka ta kudu. Samer shi ne Babban Manaja kuma Shugaba na BCI Technologies CA na tushen Venezuela, an kuma nada shi bisa ga dokar E.O. 13224, kamar yadda aka gyara, a matsayin mai mallakar, sarrafawa, ko jagora, kai tsaye ko a kaikaice.

Dan Amer Mahdy Akil Helbawi, a madadin Amer, yana gudanar da ayyukan kasuwanci a Colombia. Shi ne Babban Jami’in Gudanarwa na kamfanin Zanga S.A.S., wanda ya kasance babban mai samar da kayayyaki ga kamfanoni da daidaikun mutane a cikin wannan kungiyar, ciki har da Amer. An sanya wa kamfanin Zanga S.A.S takunkumi saboda mallakar Helbawi ne.

Kamfanin Black Diamond SARL na Lebanon ya sami kusan dalar Amurka 40,000 daga hanun Zanga S.A.S. Ana sanya masa takunkunmi saboda taimakon kayan aiki, tallafi, ko bayar da tallafi ko kaya ko ayyuka na kamfanin Zanga S.A.S. An kuma nada Ali Ismail Ajrouch a matsayin mai mallakar ko jagoran kamfanin Black Diamond SARL.

"Ayyukan yau ya jaddada kudurin gwamnatin Amurka na bin jami'an Hizballah da masu tallafa masu a duk inda suke," in ji karamin sakataren baitul malin ta'addanci da leken asiri, Brian E. Nelson.

"Za mu ci gaba da kawar da wadanda ke neman yin amfani da tsarin hadahadar kudade na Amurka da na kasa da kasa don samar da kudade da kuma shiga ayyukan ta'addanci."

XS
SM
MD
LG