Accessibility links

Breaking News

Shugaba Biden Da Xi Na China Sun Bude Hanyoyin Tattaunawa


Shugaban Amurka Joe Biden, (dama) da takwaran aikinsa na China, Xi Jinping, hagu, yayin da suka hadu bayan taron Asia-Pacific a jihar California a ranar 15 ga watan Nuwamba, 2023.
Shugaban Amurka Joe Biden, (dama) da takwaran aikinsa na China, Xi Jinping, hagu, yayin da suka hadu bayan taron Asia-Pacific a jihar California a ranar 15 ga watan Nuwamba, 2023.

Shugaba Biden ya bayyana cewa, shi da shugaba Xi sun kuma yi musayar ra’ayoyi kan batutuwa da dama da su ka shafi duniya, ciki har da yakin da Rasha ke yi da Ukriane da rikicin Gaza.

“Ci gaba” ita ce muhimmiyar kalmar da shugaba Joe Biden ya yi amfani da ita don kwatanta ganawarsa da shugaban kasar China Xi Jinping. Shugabannin biyu sun gana a karon farko cikin shekara guda a gefen babban taron habaka tattalin arzikin kasashen yankin Fasifik na Asia.

“Na yi amanna cewa a yau, da muka dora daga kan tubalin babbar tattaunawar difilomasiyya da muka shimfida tsakanin bangarorinmu a cikin watanni da dama da su ka gabata, mun sami wani muhimmin ci gaba.

Batu na farko na yarjejeniyar da shugaba Biden ya ambata shi ne sake soma hadin gwiwa kan yaki da miyagun kwayoyi, musamman game da sinadarai da kayan aikin da ke amfani da su wajen samarwa da rarraba maganin fentanyl mai hatsarin gaske.

“Muna daukar matakai don rage yawan kwararar sinadarai da kwaya daga China zuwa yammacin dunniya. Hakan zai ceci rayuka, kuma na yaba da jajircewar shugaba Xi kan wannan batu. Ni da shugaba Xi mun dora wa tawagoginmu alhakin su kiyaye manufofi da kuma bin doka da oda don tabbatar da yarjejeniyar ta yi aiki kamar yadda ya kamata.”

Bangare na biyu na yarjejeniyar, wanda shugaban ya kira “mai matukar mahimmanci,” shi ne maido da babbar alakar rundunar soja.

"Mun dawo da tuntuba da sadarwa ta kai tsaye. Rashin fahimta daga kowane bangare zai iya haddasa damuwa tare da kasa kamar China ko wata babbar kasa. Don haka, ina ganin mun samu ci gaba sosai a can ma.”

Na uku,shugbannin biyu sun amince kwararunsu su hadu domin tattaunawa kan batutuwan hatsari da matakan kariya masu alaka da fasahar zamani ta samar da bayanan sirri. Wadannan muhimman matakai ne a kan madaidaiciyar hanya,” in ji Shugaba Biden,” don sanin abin da ke da amfani da abin da ba shi da amfani da kuma abin da ke da hatsari da abin da ba za’a amince da shi.”

Shugaba Biden ya bayyana cewa, shi da shugaba Xi sun kuma yi musayar ra’ayoyi kan batutuwa da dama da su ka shafi duniya, ciki har da yakin da Rasha ke yi da Ukriane da rikicin Gaza.

“Kuma kamar yadda nake yi a koyaushe, na bijiro da wuraren da Amurka ke da damuwa game da ayyukan kasar China, ciki har da ‘yan Amurka da aka tsare da kuma hana su fita, da 'yancin bil adama da ayyukan tursasawa a tekun kudancin China. Na kuma jaddada mahimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashingin Taiwan.”

Shugaba Biden ya ce gamawar da Shugaba Xi ya nuna wa duniya wani muhimmin al’amari na diflomasiyyar Amurka: “Muna tattunawa da abokanan gasarmu. Magana ta keke-da-keke da juna, ta yadda babu wata rashin fahimta shi ne muhimmin bangare na wanzar da zaman lafiya a duniya, da cika alkawari ga mutanen Amurka."

XS
SM
MD
LG