Kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a duniya na G7, wadanda sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kira "kwamitin gudanarwa na dimokiradiyya mafi ci gaba a duniya," sun kammala taronsu a tsibirin Capri na Italiya.
Sakatare Blinken ya ce ministocin harkokin wajen sun fito "da karfin hadin kai fiye da na kowane lokaci" kan muhimman kalubalen da ke gaban kasashen duniya, da suka hada da rikici a Gabas ta Tsakiya, da cin zallin da Rasha ke yi wa Ukraine, da kuma tabbatar da budewa da 'yanci Indo-Pacific:
“Na farko G7 sun yi Allah wadai da harin da Iran ta kai wa Isra’ila, wanda babu ma’ana. Mun himmatu ga tsaron Isra'ila. Mun kuma kuduri aniyar rage tashin hankali, don kokarin kawo karshen wannan tashin hankalin."
Don ganin gwamnatin Iran ta dauki nauyin ayyukanta na ta da zaune tsaye, Amurka ta ba da sanarwar karin takunkumi kan makamai masu linzami na Iran da karfin su, kuma kasashen G7 za su sa karin takunkumi.
Ministocin harkokin wajen sun kuma “mai da hankali sosai” kan Gaza, don nuna goyon bayan tsagaita bude wuta nan take tare da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su. Hamas, duk da haka, ta yi watsi da "shawarwari masu karinci daga Isra'ila," in ji Sakatare Blinken, kuma "da alama sun fi sha'awar rikicin yankin.
"Yana ci gaba da motsa ginshiƙan manufofi, kuma duniya na buƙatar sani kuma tana buƙatar fahimtar, cewa kawai abin da ke tsakanin tsagaita wuta da al'ummar Gazan shi ne Hamas."
Game da cin zarafi da Rasha ke yi na Ukraine, G7 ta bayyana "a fili" goyon bayan da take baiwa Ukraine, in ji Sakatare Blinken. "Putin yana tunanin cewa zai iya fin karfin Ukraine kuma ya fi karfin magoya bayan Ukraine."
“Saƙon da ke fitowa daga Capri shi ne: Ba zai iya ba. Kowane mamba na G7 yana ba da gudummawa ta musamman ga tsaron Ukraine. "
Wani muhimmin abin da taron ya mayar da hankali a kai shi ne makasudin ‘Yanci dabudewar indo-Pacific.
“G7 sun haɗa kai kan buƙatar zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigar Taiwan, tekun Kudancin China, Koriya ta Kudu, da kuma hadin kai ɗaya don tinkarar ayyukan rashin adalci na China da rashin adalcin kasuwanci, musamman idan aka yi la’akari da abin da ya shafi kayayyyaki da ke cika kasuwannin kasashenmu da sabbin kayayyaki da fasahohin da ake ba su tallafi mai yawa da kuma rage farashi, suna fitar da namu kayayyakin kasuwanci daga kasuwanninmu da kuma neman mamaye kasuwannin da kansu.”
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Blinken ya jaddada cewa, abu mafi daukar hankali game da kungiyar G7, "shi ne babban haɗin kai a cikin hanyoyinmu ga waɗannan ƙalubalen, haɗin kai tsakanin Amurka, Turai, da abokan hulɗa a Asiya."
Wannan sharhi ne da ke bayyana ra'ayoyin Gwamnatin Amurka.