Tukwici Ga Duk Wanda Ya Ba Da Bayani Kan Abukar Ali Adan

Tsohon Hoto: Shugaba Biden

Gwamnatin Amurka na yi tayin tukwicin dala miliyan $5M ga duk wanda ya bayar da bayanai da za su kai ga gano ko kuma wurin da Abukar Ali Adan yake.

Adan shi ne mataimakin sarki, ko shugaban kungiyar al-shabab ta ‘yan ta’adda. Bayan shafe shekaru da dama yana jagorantar shugabancin reshen sojojin al-Shabab na Jabhat, ya kuma karbi mukamin babban hafsan soji na kungiyar, kuma a hankali an daga darajarsa zuwa matsayin da yake na mataimakin shugaban kungiyar.

Kungiyar Al-shabab ita ce mafi girma kuma mafi samun kudi da ke da alaka da kungiyar masu tsatstsauran ra’ayi ta al-Qa’ida, a cewar Majalisar Dinkin Duniya. Al-shabab wadda ke da mazauni a Somaliya kuma tana aiki ne a gabashin Afirka, tana kuma kai hare-hare a Somaliya da makwabtanta Kenya da Habasha, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane da rauntasu wasu da dama.

A watan Janairun 2018, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Abukar Ali Adan a matsayin dan ta’adda na duniya karkashin dokar shugaban kasa mai lamba 13224, wadda ke kakaba takunkumi mai tsauri kan mutanen kasashen waje da aka amince sun aikata ko haifar da babbar barazanar aikata ayyukan ta’addanci da ke barazana ga tsaron Amurkawa ko tsaron kasa da manufofin kasashen waje ko tattalin arzikin Amurka.

Bugu da kari, Adan yana cikin jerin takunkumin dokar Majalisar Dinkin Duniya ta 1844, saboda shiga ko bayar da tallafi ga ayyukan da ke barazana ga zaman lafiya da tsari ko zaman lafiyan Somaliya da dakarun wanzar da zaman lafiya.

Idan kai ko wanda ka sani yana da bayanin inda Abukar Ali Adan yake, sai a tuntubi “Reward for Justice” ta hanyar manhajar Telegram ko WhatsApp ta wannan lamba, +1-202-702-7843, duniya ko ta wannan lamba +254-718712366 a Kenya da +252-684343308 a Somaliya. Ana iya samun karin bayani game da wannan tayin tukwicin a internet a shafin Reward for Justice, wanda aka rubuta kamar haka, www.rewardsforjustice.net .

Za’a bincikai duk rahotannin masu inganci da aka samu, kuma za’a sakaya sunayen dukkan wadanda suka b da bayanan.

Yekuwa kenan da gwamnatin Amurka ta fitar.