Accessibility links

Breaking News

Amurka Ta Yabawa Kotun ICC Kan Yadda Take Tabbatar Da Adalci


Shugaban Amurka, Joe Biden
Shugaban Amurka, Joe Biden

Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC, ita ce kawai kotun kasa da kasa ta dindindin mai hurumin gurfanar da mutane kan laifukan kisan kare dangi, laifuffukan cin zarafin bil adama, laifuffukan yaki da kuma laifin wuce gona da iri. A karshen watan Oktoba, shugaban kotun ta ICC ya gabatar da rahoton shekara-shekara ga Majalisar Dinkin Duniya. A wannan shekara, cibiyar a shekararta ta ashirin,ta ciri tuta, inda take sauraren kararraki biyar.

Kotun ta ICC na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da adalci a mataki na kasa da kasa, in ji Wakilin Amurka ga Majalisar Dinkin Duniya, Andrew Weinstein. "ICC ta samu ci gaba wajen dabbaka adalci ga wadanda abin ya shafa a duniya."

"Ayyukan ICC ke yi a duniya, suna nuna muhimmiyar rawar da take takawa a matsayin wata kafa da ake tabbatar da an hukunta masu laifi, ko da a ce abin kan dauki tsawon lokaci.”

Daga cikin muhimman shari’o’in da kotun ta ICC ta gudanar a wannan shekarar, har da shari’ar kwamandan Janjaweed [Ali Mohammed Ali Abd-al Rahman] da aka fi sani da Ali Kushayb. Wannan dai ita ce shari'a ta farko da ake yi wa duk wani babban shugaba bisa laifukan yaki da cin zarafin bil'adama da gwamnatin tsohon shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ta aikata a kan al'ummar Darfur.

Kazalika, kotun ta ICC ta yi aiki kafada da kafada da gwamnatin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, domin gurfanar da Alfred Yekatom, Patrice Ngaisonna, da Mahamat Said Abdel Kani a gaban kuliya bisa laifukan cin zarafin bil'adama da laifukan yaki.

Shari'ar wata manuniya ce ga masu yi wa doka karar tsaye.

"Waɗanda ke ƙarƙashin sammacin kama su daga ICC, to dole ne su fuskanci shari'a a gaban shari'a ta gaskiya, mai zaman kanta, da kuma sahihin shari'a."

A wannan lokaci dole ne mu magance "mummunan yakin da ake yi a Ukraine, inda fararen hula ke fuskantar munanan hare-hare a kullum daga sojojin Rasha," in ji Weinstein.

“Amurka na goyon bayan bincike da dama na kasa da kasa kan ta’asar da ake yi a Ukraine, ciki har da wadanda kotun hukunta manyan laifuka ta ICC, da Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar tsaro da hadin gwiwa a Turai suka gudanar. Za mu ci gaba da tsayawa tare da Ukraine domin fuskantar zaluncin Rasha da kuma tabbatar da an hukunta masu laifi.

Weinstein ya ce "Adalci ba wai abu ne da ake kallonsa a matsayin dole ba ne kawai, amma yana da mahimmanci don kiyaye zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa."

“Amurka na babbar mai goyon bayan duk wani abu da zai tabbatar da adalci ga wadanda aka zalunta. Wadannan su ne muhimman abubuwa, da za a iya cin ma ta hanyar hadin kai, kuma kotun ta ICC wani sashe ne da za hada kai da shi wajen tabbatar da adalci.

XS
SM
MD
LG