Accessibility links

Breaking News

Afirka Da Batun Sauyin Yanayi: Nahiyar Da Ta Fi Fuskantar Barazana


 Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield
Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield

Babu shakka, “Afirka na dauke da kasashe 17 da suka fi fuskantar barazanar sauyin yanayi, kamar yadda Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas Greenfield ta fada a watan Oktoban 2022.

Idan tashi maganar matsalar sauyin yanayi, ana kallon Afirka a matsayin nahiyar da ta fi fuskantar barazana idan aka kwatanta da sauran sassan duniya.

“Muna gab da fadawa kangin matsalar sauyin yanayi.” In Sakataren harkokin wajen Amurka, Antonio Guterres. Rawar da nahiyar Afirk take takawa wajen haifar da matsalar dumamar yanayi, ba ta taka kara ta karya ba. Amma kuma ita ta fi shafuwa da wannan matsala.”

Babu shakka, “Afirka na dauke da kasashe 17 da suka fi fuskantar barazanar sauyin yanayi, kamar yadda Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas Greenfield ta fada a watan Oktoban 2022.

“Sauyin yanayi na barazana ga rayuka da hanyoyin biyan bukatun miliyoyin mutane a Afirka. Matsalar na ta’azzara matsalar ficewa da mutane suke yi a muhallansu, da kara durkusar da kasashen da suke fama da matsalar tattalin arziki, shugabanci da tsaro. Sannan wannan matsala ta sauyin yanayi, ita ce kan gaba wajen haifar da matsalar karancin abinci a nahiyar. Sauyin yanayi, na nufin rashin samun amfani gona mai kyau ga manoma. Hakan kan rage abin da ake girba da kashi 40 a yankin kasasne da ke yamma da Saharar Hamada.”

“Matsalar sauyin yanai, batu ne da ya shafi duniya baki daya, wacce ke bukatar masalahar gaggawa. “ In ji Thomas Greenfield. “Sannan,kalubale ne da ke bukatar dukkanmu, mu dauki matakan samar da makamashi masu tsafta a kasashenmu.”

Hakan ya kasance ne, saboda mun san cewa sakamakon matsalar sauyin yanayi shi ke haifar da husuma.

“Idan yankunan da ke fama da matsalar rikici ko rashin tsaro suka kuma fuskanci matsalar rashin abinci da tauyewar tattalin arziki, sai yiwuwar samun tashin hankali ya karu. Sannan fari, amabliyar ruw, gobara, da matsanancin yanayi su sa samun abinci da tattalin arziki mai kyau su gaza samuwa bayan da cikas da zu haifar wajne tabbatar da zaman lafiya.

“Wadannan matsaloli, cakude da rikicin siyasa, da rashin tsaro, na sa iyalai da ba su da zabi cikin kangin rayuwa yayin da suke kokarin nemawa kansu abinci. In ji Ambasada Thomas Greenfield.

“Dalili kenan da ya sa Amurka karkashin shirin nan na ciyarwa, ta kuduir aniyar kashe dala biliyan biyar cin shekaru biyar masu zuwa, don a karfafa hanyoyin samar da abinci mai gina jiki a duniya.

Kasashe 16 daga cikin kasashen da shirin ciyarwa na ‘Feed the Future’ya sag aba, daga Afirka suke, kuma wannan shiri zai taimakawa sassan Afirka da manoma wajen lakantar hanyoyi zamani da za su samu amfani gona mai kyau. A lokaci guda kuma, muna aiki don tallafawa mutum rabin biliyan a kasashe masu tasowa don horar da su yadda za su magance matsalar sauyin yanayi karkashin wannan shiri.

“Bari sake sabunta alkawarinmu na ganin mun yi aiki tare da ku….. don samar da tsaftataccen makamshi da tattalin arziki mai dorewa. Wanda zai taimakawa dumbin arzikin Afirka, wajen magance matsalar sauyin yanayi.

XS
SM
MD
LG