Accessibility links

Breaking News

Amurka Ta Saka Takunkumi Kan Kungiyoyin Da Ke Safarar Makamai A Gabashin Afirka


Biden ASEAN

Amurka za ta ci gaba da yin aiki tare da kawayenta a gabashin Afirka domin dakile hanyoyin da ISIS da al-Shabaab ke samun kudadensu, a wani mataki na kassara wadannan kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Kungiyoyin 'yan ta'adda da ke aiki a gabashin Afirka na ci gaba da yin barna a Somalia, inda suke kai hari kan fararen hula, da ma'aikatan gwamnati, da masu kai daukin farko don sanya tsoro a zukatan mutane. A ranar 29 ga Oktoba, al-Shabaab ta dauki alhakin wani mummunan harin bam da aka kai a Mogadishu wanda ya lakume rayuka sama da 100 tare da jikkata fararen hula kusan 300.

Karamin Sakataren Baitulmali da ke kula da kudaden yaki da Ta'addanci da Leken Asiri na Kudi, Brian Nelson ya mika ta'aziyyarsa "ga duk wadanda suka rasa 'yan uwansu kuma suka jikkata a wannan mummunan harin tare da yin Allah wadai da wannan aikin ta'addanci."

A cikin martani, Amurka ta ɗauki “aniyyar kassara cibiyoyin da ke samarwa da kungiyar ISIS- reshen Somalia da al-Shabaab wadanda ke tallafawa ayyukan ta'addancin."

Amurka ta ayyana kungiyar ISIS da Somaliya na masu safarar makamai, abokan huldarsu, da kuma wata huldar kasuwanci da ke taimaka wa kungiyoyin ta’addanci.

Wadannan kungiyoyi suna aiki ne tsakanin Yemen da Somalia kuma suna da alaka mai karfi da al-Qaida a yankin Larabawa.

Ma'aikatar Baitulmali ta sa ido kan wani muhimmin mai goyon bayan ISIS a Brazil, Osama Abdelmongy Abdalla Bakr.

A 2016, manyan shugabannin ISIS sun umarci Bakr da ya samo makamai da kayan aikin soja ga kungiyar ta'addanci.

Shigar wadanda aka ayyana a wasu ayyukan aikata laifuka da suka hada da satar fasaha da kamun kifi ba bisa ka'ida ba, ya nuna irin yadda kungiyar ISIS da Somaliya ke hade da haramtattun kungiyoyin 'yan ta'adda da ke aiki a yankin.

Ma'aikatar Harkokin Wajen ta ayyana ISIS-Somalia a ranar 27 ga Fabrairu, 2018, da kuma Abdiqadr Mumin, shugaban ISIS-Somalia, a ranar 11 ga Agusta, 2016, a matsayin 'yan ta'adda na musamman da aka zayyana a duniya bisa ga umarnin zartarwa na 13224. ISIS ta ƙara kaimi wajen neman kudaden shiga a Gabashin Afirka. ISIS-Somalia, wacce ke ci gaba da kai hare-haren ta'addanci kan fararen hula, tana ci gaba da samun yawancin kudaden da take samu ta hanyar karba a wajen al'umomin yankunan domin samun kudade da daukar masu mata aiki.

Kungiyar tana azabtarwa, tsoratarwa, da kuma kashe 'yan kasuwa da fararen hula na Somaliya wadanda ba sa tallafa mata da kudi ko samar da kayayyaki.

Amurka za ta ci gaba da yin aiki tare da kawayenta a gabashin Afirka domin dakile hanyoyin da ISIS da al-Shabaab ke samun kudadensu, a wani mataki na kassara wadannan kungiyoyin ‘yan ta’adda.

XS
SM
MD
LG