A tsakiyar watan Satumba, Hukumar raya kasashe masu tsowa ta Amurka USAID, gwamnatin Norway, da dandalin tattalin arzikin duniya, sun shirya wani zama a gefen babban taron Majalisar Dinkin Duniya, domin tattauna yadda za a taimaka wajen samar da kudaden bunkasa noma a Afirka, da kuma nemo sabbin hanyoyin tallafa wa masu ruwa da tsaki a harkar noma, sarrafa amfanin gona, da sayar da abinci ga mutane ke ci.
Bangaren noma ne ke samar da kashi biyu bisa uku ne na ma'aikatan Afirka. Amma duk da haka, wannan nahiya mai saurin bunkasuwa, wadda ake sa ran za ta kai kashi daya bisa hudu na yawan al'ummar duniya nan da shekara ta 2050, har yanzu ba ta noman isasshen abinci da za ta ciyar da al'ummarta, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana manufar ci gaba mai dorewa na biyu: Kawar da Yunwa baki daya.
Kawar da yunwa na ɗaya daga cikin manyan manufofin Hukumar Raya Ƙasashe masu tasowa ta Amurka, USAID. "Muna mai da hankali sosai kan inganta hanyoyin samar da kananan manoma, musamman wadanda ke samar da mafi yawan abinci a nahiyar Afirka, wajen taimaka musu don samun karin kayan aiki," in ji Isobel Coleman, mataimakiyar shugaban tsare-tsare ta hukumar ta USAID.
“Iri. Taki. Samar da kudade. Taron na daren yau shi ne game da haɓaka hanyoyin samar da kudade - ba wai ƙaramin kudi ba, kudi mai yawan gaske. ”
Wadannan sana’o’in noma ne wadanda suka wuce bukatar samar da kanannan kudade, amma wadanda ba su kai yin aiki da manyan bankuna ba.
"Masu zuba hannun jari suna kallon ... zuba jari a aikin noma a Afirka a matsayin wani abu mai cike da kasada," in ji Isobel Coleman.
Wannan ne ya sa Hukumar ta USAID ta kaddamar da Asusun Tallafawa Kananan Matsakaictan Kamfanoni na Aikin Noma a Afirka, wanda ke da damar tallafawa kananan masana’antu 500 da kuma kananan manoma miliyan 1.5. An yi shi da niyyar “taimakawa wajen rage hatsari ga masu zuba jari, don taimakawa ta hanyar sanya kudaden tallafi, tare da wasu kudade na tallafi daga gwamnatin Norway," in ji Coleman. "Burin mu shi ne, mu fara da dala miliyan 70 amma mu samu akalla dala miliyan 200."
"Idan kamfani ya shiga cikin wata matsala, asarar za ta fara fadawa kan wannan kuɗin masu ba da gudummawa. Za mu dauki asarar farko. Don haka, zai taimaka wa kamfanonin da za su kara zuba jari, suna yin amfani da jarin kamfanoni masu zaman kansu, su ce, ‘alal misali, za su yi asara ta farko.’ Don haka ya rage musu hatsarin jarin. Kuma muna fatan wannan zai haifar da ƙarin kudade. "
"Muna iya kokarin nemo dala biliyan 1 na kudade don samun damar taimakawa wasu kananan manoma su bunkasa kasuwancinsu, don hakan ya yi tasiri sosai a tsarin da sauran sassan fannin na noma a Afirka cikin shekaru masu zuwa.”