Harin rashin adalci na Rasha da take kaiwa kan karamar makwabciyarta, Ukraine, ya yi tasiri a fadin duniya, ba wai don harin da Rasha ta kai wa makwabciyarta mai zaman lafiya ba, amma saboda “ya tsananta matsalar rashin abinci da duniya tuni take fama da shi daga tasirin annobar COVID-19 da sauyin yanayi da kuma yake-yaken yankuna,” in ji mataimakiyar Shugabar Shirin USAID na Feed the Future, Dina Esposito.
Dina Esposito ta ce “Wannan yakin da ake yi tsakanin manyan masu fitar da abinci da taki da albarkatun man fetur ya fallasa dogaro ga wasu tsirarun kasashe masu fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje don ciyar da duniya, da kuma nuna rauni na wasu kasashe masu shigo da abinci.”
“Martanin gwamnatin Amurka ya nuna rikicin bangarorin biyu, a bangare guda, muna ba da tallafin da ba’a taba gani ba ga al’ummar Ukraine, yayin da muke kara kaimi wajen dakile illolin rashin abinci da farashin taki, musamman ma a kasashen masu rauni.”
Daga cikin wadanda suka fi fama da matsalar akwai kasashe a Afirka,” in ji mataimakiyar shugaba Esposito. “Ta hanyar taimakon abinci da hadin gwiwar shirin Feed Future, USAID ta kasance cikin kyakkyawan wuri to mayar da martani ga tasirin yakin da ke haifar da yunwa da rashin abinci maigina jiki a cikin kasashen da yafi shafa sosai na farashin abinci da taki.”
“Mun kara yawan tallafi don tabbatar da cewa miliyoyin manoma sun sami ingantaccen tiri, taki, ingantattun hanyoyin samar da kayayyaki, da kuma samar da kudade don taimaka wa wajen daidaita farashin da ya yi sama da ya kafa tarihi na kayan masarufi da yawa.
“Mun taimaka wajen ci gaba da bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu, masu mahimmanci ga tattalin arzikin noma, wanda ke ci gaba da gudana. Sannan mun inganta hanyoyin samar da tsaro da ayyukan abinci mai gina jiki ga mata da yara masu rauni.”
Kazalika, hukumar USAID na kokarin fadada ayyukan noma na gida da na yanki da kasuwanni. “Amurka na ba da tallafin fasaha ga cibiyoyin yanki don taimaka wa nahiyar ta amince da Kasuwanci Nahiyar Afirka Mara Shinge na Yanki,” in ji Esposito.
“Har ila yau, muna iaki kai tsaye tare da kasashen Afirka da kuma hadin gwiwar jami’o da yawa na Afirka da kuma tunani da yawa don taimakawa kasashen wajen samar da ingatattun manufofi da tsare-tsare masu inganci wadanda za su hada manayan kasuwannin yanki, da kuma habaka zuba jarin kamfanoni masu zaman kansu da kuma saka hannun jarin gwamnati masu a wurare masu muhimmanci kamar bincike, fadada ayyuka da ababen more rayuwa.”
“Mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ta girgiza tsarin samar da abinci a fadin duniya,” in ji Mataimakiyar Shugaba Esposito.
“Yayin da hoton yunwa na duniya ya zama kalubale da za’a fadi akalla, akwai kuma kakkarfan tasirin da yuwuwar wadannan wurare da galibi ana rarraba su kamar “yunwa.”