Accessibility links

Breaking News

Illolin Da Yakin Rasha Ke Haifarwa


Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden

Yayin da wasu sassan Afirka da Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da fuskantar matsalar karancin abincin da ba a taba ganin ba irin ta ba, Rasha ta dakile ayyukan noma a Ukraine tare da hana aikawa da kayan abinci zuwa sassan duniya ta tekun Bahr Al Aswad.

Babu haufi cewa haramtaccen yakin da Rasha ke yi a Ukraine, ya haifar da dumbin matsaloli a sassan duniya.

Hatta kasashen da babu ruwansu a wannan yaki na dandan kudarsa.

Mamayar da Rasha ta yi, ta haifar yi mummunan tasiri akan fannin samar da makamashi a kasuwannin duniya, kuma tana daya daga cikin dalilan da suka sa tattalin arzikin duniya ya yi tafiyar hawainiya a bara, inda aka ci gaban maki 3.1 a cewar rahoton da hukumar kula da tattalin arzikin da ci gaba ta fitar a watan Nuwamban 2022.

Wani babban abin tashin hankali shi ne, yadda mutanen da ke bukatar tallafin abinci suka shiga mummunan yanayi.

Yayin da wasu sassan Afirka da Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da fuskantar matsalar karancin abincin da ba a taba ganin ba irin ta ba, Rasha ta dakile ayyukan noma a Ukraine tare da hana aikawa da kayan abinci zuwa sassan duniya ta tekun Bahr Al Aswad.

Sai dai babu wanda ya jigita daga wannan yaki kamar al’umar kasar ta Ukraine, wadanda suka fadi kangin mamayar dakarun Rasha tun da aka fara yakin.

Cikin watanni 14 da suka gabata, ofishin kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce fararen hula kusan dubu 24 aka kashe.

Ko da yake, ofishin na UNHCR ya ce akwai yiwuwar adadin ya fi haka yawa.

“Babu wadanda suke dandan kudarsu kamar al’umar Ukraine,” in ji Wakili na musamman kan sha’anin siyasa a Majalisar Dinkin Duniya Ambasada Robert Wood.

Ya kara da cewa, “bayan watanni 15… har yanzu, babu alamar za a kawo karshen matsalar da jama’a suka shiga, sanadiyyar yakin da Rasha ta far aba tare da takala ba. Maimakon haka, adadin mutanen da ke mutuwa sanadiyyar hare-hare makamai masu linzami da jirage mara matuka akan fararen hular Ukraine sai kara karuwa yake.”

A cewar Wood, “Tun daga watan Mayu, Rasha ta kaddamar da hare-haren sama sama da 145 a cikin Ukraine. Hakan na nufin, an harba makami mai linzami ko jirgi mara matuki ko an jefa bam daya a kowace sa’a guda cikin sa’a 24 a kwanaki uku ba tare da kakkautawa ba.

Cikin wadannan kwanaki uku kadai, hare-haren Rasha sun kashe tare da jikkata fararen hula sama da 100 ciki har da akalla yara biyar.”

A lokaci guda, “kungiyiyi ba da agaji, sun ba da rahyon cewa, ana fuskantar matsalar karancin wutar lantarki, abinci, man fetur a yankunan da ke goshin yakin,” a cewar Ambasada Wood.

“Hare-haren da Shugaba (Vladimir) Putin yake kai w akan muhimman wurare na barzana ga dukkan mu baki daya….. Rasha ba ta da burin daukan matakan magance tsirin yakin Ukraine duba da yadda yakin yake shafar wasu yankunan duniya, idan aka yi la’akkari da yadda ta yi kememe wajen ganin an sasanta rikicin ta hanyar diflomasiyya.”

“Muna sake kira ga rasha da ta kawo karshen hare-haren da take kai w akan al’umar Ukraine, ta kuma janye dakarunta daga sassan kasar baki daya. Rasha ita kadai za ta iya kawo karshen wannan yaki mar akan-gado da ta fara.” In ji Ambasada Wood.

SANARWA: Wannan Sharhi matsayar Gwamnatin Amurka yake bayyanawa.

XS
SM
MD
LG