Afirka Ce Nahiyar Da Ya Kamata A Yaki Matsalar Sauyin Yanayi

Jakadan Amurka na musamman kan yaki da sauyin yanayi, John Keryy a taron Sauyin yanayi na Afirka da aka yi a Nairobi, Kenya (Photo by Luis Tato / AFP)

 “A yanzu Shugaba Biden ya kaddamar da wani shiri mai suna Shirin Shugaban Kasa na Gaggawa don rungumar sauyi, kuma ya yi alkawari cewa za mu taimakawa akalla rabin biliyan mutane a kasashe masu tasowa, musamman a Afirka"

Idan ana maganan kan tasirin Sauyin Yanayi, “daga cikin kasashe 20 da suka fi illatuwa a Duniya, 17 a Afirka suke,” in ji jakadan Amurka na musamman kan yanayi John Kerry.

Da yake jawabi a taron yanayi na Afirka na 2023 a Nairobi, Kenya, Kerry ya ce, "wannan matsalar da muke fuskanta, mutum ne yake haddasa ta. Batun ne da ya shafi gurbta muhalli.”

Lallai, Afirka tana kan gaba a fuskanta matsalar yanayi, Wanda "Ƙona Man Fetur ne ke haddasawa." "Kasashe 20 ne ke samar da kashi 80 cikin 100 na duk hayakin da ake fitarwa," in ji Mr. Kerry. "Yana da Mahimmanci Ga Dukkanin waɗannan ƙasashe 20 da su ɗauki matakai nan da nan don samun shiga cikin yarjejeniyar Paris."

“Idan har Adalci zai zama mai ma’ana, tabbas yana nufin cewa idan za'a yi sauyi, kowa na iya cin moriyar Fa'idodin sauyi. A halin yanzu, a bayyane yake cewa ba za ku iya magana game da sauyi ba, amma ga wasu mutane ,babu sauyi ko kadan, ga wasu mutane kuma akwai basussuka mara adalci da ma ya ka fi karfin duk wani zabin da waɗannan ƙasashen za su yi. "

Canji shi ne Mabuɗin Rayuwa. “Kowanne kwanaki 18, muna da taron da ya shafi yanayi na dala biliyan 1 a wani wuri a wannan duniyar. Don haka, sauyi yana da mahimmanci, ”in ji John Kerry.

“A yanzu Shugaba Biden ya kaddamar da wani shiri mai suna Shirin Shugaban Kasa na Gaggawa don rungumar sauyi, kuma ya yi alkawari cewa za mu taimakawa akalla rabin biliyan mutane a kasashe masu tasowa, musamman a Afirka, don samun damar dacewa ga tasarin duk wani mummunan yanayin."

Mr. Kerry ya sanar da cewa, Amurka za ta ba da karin dala miliyan 20 ga shirin daidaita al'amura a Afirka don inganta samar da abinci, wanda zai zuba jari a harkokin kasuwancin noma. Wasu karin dala miliyan 10 za su je wurin sauyin yanayi, sarrafa kudi wajen ƙirƙirar fasaha domin samun ci gaba kamar ta fannin adana abinci cikin sanyi.

"Mun koyi cewa daidaitawa yana ceton rayuka, yana samar da ayyuka, kuma babu shakka wannan amfanin kwakwlawa ne kawai Hanyoyi da gadajen da aka gina a yau za su iya taimakawa ci gaba da dakatar da talauci idan har suna tsaye gobe”.

"Afrika tana fama da babban Mummunan Tasirin bala’in Yanayi," in ji Kerry. "Yana da muhimmanci kowace ƙasa ta tashi tsaye don taimakawa sauran ƙasashe, musamman Afirka a wannan lokacin, don samun damar tunkarar matsalolin da sauyi yanayi ke haifarwa.