"Saboda haka, a bayyane yake shirye-shiryen Isra'ila na biyan bukatun mutanen da suka rasa matsugunansu ba su wadatar ba." in ji Ambassador Wood.
“Waɗannan mutane biyu ne da ake zargi da hannu a kisan kiyashin da aka yi a Rwanda a shekara ta 1994. Don haka, har yanzu ana bayar da tukwici ga bayanan da za su kai ga kama su.”
“Muna kira ga Vietnam da ta mutunta ‘yancin fadin albarkacin baki, tarayya, da addini ko imani." Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ya ce.
Amurka ce kasar da ta fi taimakawa Haiti, in ji Mataimakin Sakatare Nichols. "Amma sauran kasashe da kungiyoyin kasa da kasa su ma ana bukatar su kara himma wajen bayar da taimako,"
“Saƙon da ke fitowa daga Capri shi ne: Ba zai iya ba. Kowane mamba na G7 yana ba da gudummawa ta musamman ga tsaron Ukraine. "
Don tabbatar da samar da muhimman ayyuka ga al'ummar Libya da kuma rarraba kudaden shiga cikin adalci, yana da muhimmanci kasar ta samar da kasafin kudin na bai daya da kuma daukar matakan daidaita kudaden, in ji Ambassador Wood.
"Maganar gaskiya daya ce kacal a nan, ita ce a ajiye bindigogin." In ji Perriello.
Amurka ta sake yin kira ga gwamnatin Sudan ta Kudu, da ta yi zabin da ya dace. Shekaru 12 bayan samun ‘yancin kai, lokaci ya wuce da gwamnatin rikon kwarya za ta bude sabon babi.
Idan kai ko wanda ka sani yana da bayanin inda Abukar Ali Adan yake, sai a tuntubi “Reward for Justice” ta hanyar manhajar Telegram ko WhatsApp ta wannan lamba, +1-202-702-7843, duniya ko ta wannan lamba +254-718712366 a Kenya da +252-684343308 a Somaliya.
Load more