Accessibility links

Breaking News

An Dauki Hanyar Kawo Karshen Rikicin Haiti


Mataimakin Sakatare, Brian Nichols
Mataimakin Sakatare, Brian Nichols

Amurka ce kasar da ta fi taimakawa Haiti, in ji Mataimakin Sakatare Nichols. "Amma sauran kasashe da kungiyoyin kasa da kasa su ma ana bukatar su kara himma wajen bayar da taimako,"

An dauki kwararan matakai na kwantar da tarzoma da hargitsi a Haiti a karshen watan Afrilu lokacin da aka rantsar da kwamitin rikon kwarya a fadar shugaban kasa a birnin Port-au-Prince.

Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin yammacin duniya Brian Nichols ya ce, "shigar da majalisar shugaban kasar ta rikon kwarya mataki ne mai matukar muhimmanci ga hanyar Haiti na zuwa ga mulkin dimokiradiyya, sabbin zabuka da inganta tsaro."

“Wannan rukunin ya ƙunshi ra’ayi mai yawa na al’ummar Haiti don neman sabuwar hanyar ci gaba. Sakamakon watannin da aka shafe ana tattaunawa tsakanin gungun masu ruwa da tsaki, kuma ina ganin lokaci ne mai kyau da inganci."

An dorawa Majalisar alhakin nada sabon Firaminista, majalisar zartarwa, da kuma hukumar zabe da za ta shirya kasar domin gudanar da babban zabe a watan Fabrairun 2026.

Matakin ya share fagen tura rundunar tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya da dama da Kenya ke jagoranta zuwa Haiti don taimakawa 'yan sandan kasar wajen magance munanan tashe-tashen hankulan gungun mutane.

Mataimakin Sakatare Nichols ya yi nuni da cewa kungiyoyin na masu ta da hankali a Haiti sun dade suna samun karfi na tsawon shekaru:

“Al’ummar Haiti ba ta iya samar da dama ga matasa ba, ayyuka, ilimi da ake bukata. Haka kuma, kasar ta Haiti ta kasance mai rauni shekaru da yawa. Yayin da tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya MINUSTAH ta fice, martabar tsaro a Haiti ta fara yin rauni, kuma tashe-tashen hankula na gungun mutane, wanda ya kasance babbar matsala tun daga shekarun 1990, da gaske ya fara girma.

Sannan, tare da kisan gillar da aka yi wa Shugaba Jovenel Moïse a watan Yulin 2021, mun ga raunin kasar da gaske wajen samar da kwanciyar hankali."

Mataimaki Sakatare Nichols ya ce, "muna fatan hakan ya inganta tsaro, tare da kasancewar tawagar taimakon tsaro ta kasa da kasa da kuma karfafa 'yan sandan kasar Haiti, tare da daukar matakai masu tsauri dangane da ci gaban tattalin arziki, shirye-shiryen karkata da ta’addanci daga jama'a, mayar da hankali kan ilimi da ayyuka a mafi yawan lokuta, yankunan da ke da rauni za su taimaka duka biyu wajen magance matsalar aikata laifuka nan take, tare da hana karin matasa shiga ayyukan kungiyoyin. "

Amurka ce kasar da tafi taimakawa Haiti, in ji Mataimakin Sakatare Nichols. "Amma sauran kasashe da kungiyoyin kasa da kasa su ma ana bukatar su kara himma wajen bayar da taimako," in ji shi. "Wannan nauyi ne na duniya, ba wai kawai alhaki ne na Amurka ba."

Wannan sharhi ne da ke nuna ra'ayoyin Gwamnatin Amurka.

XS
SM
MD
LG