Watannin bakwai da suka wuce, fatan da ake da shi na mulkin fararar hula ya gamu mummunan cikas, yayin da wani sabon rikici ya barke tsakanin rundunar sojin Sudan da dakarun sa kai na RSF.
A wani taron kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield ta bayyana yakin Sudan a matsayin “mummunan al'amari.”
“An kashe sama da mutane 5,000, sannan sama da mutane miliyan 5.7 sun tsere daga gidajensu. Babban birnin kasar, Khatoum ya tarwatse, kuma Darfur ma tana wannan rikicin na shafuwarta.”
Ambasada Thomas- Greenfield ta ce a watan Nuwamba dakarun RSF da abokansu mayakan sa kai sun yi kisan kiyashi da sauran munanan ayukan cin zarafi a yammacin Darfur.
“Shaidun sun ba da rahoton karin ayukan take hakkin bil adama a yankin yammacin Darfur, inda aka auna kabilar Masalit, da kuma tsare fararen hula ba bisa ka’ida ba da suka hada da shugabannin yankin da masu kare hakkin dan adam da masu fafutuka. A cewar likitoci da MDD, sama da mutane 800 ne aka kashe a wani hari da aka kai a Adamata, wanda ke iya zama kisan gilla mafi girma tun bayan barkewar yakin a watan Afrilu.”
Cin zarafin mata da ke da alaka da rikicin ya zama ruwan dare, ciki har da fyade, in ji Ambasada Thomas-Greenfield.
“A cewar Ofishin Hukumar Kula da Kare Hakkin Bil Adama na MDD, ana sace mata da ‘yan mata, ana daure su da rike su ba tare da son ransu ba a yankunan da ke karkashin dakarun RSF a Darfur. Wannan duk yana faruwa ne a kan idonmu. Kuma ya yi muni ga al’ummarmu baki daya.”
Dawwamammen zaman lafiya shi ne hanya daya tilo ta ceto rayuka da kawo karshen rikicin, in ji Ambasada Thomas Greenfield. Don cimma wannan manufa, Amurka tare da Saudiyya da kungiyar raya kasashe masu tasowa, sun sake gudanar da tattaunawar tsagaita bude wuta tsakanin bangarorin a Jeddah.
Rundunar soji da Dakarun RSF sun amince da nemo wuraren tuntuba don taimakawa da agaji. Bugu da kari, sun kudiri aniyar aiwatar da matakan karfafa hadin gwiwa, wadanda suka hada da samar da sadarwa tsakanin shugabannin soji da RSF, da kame wadanda suka tsere daga gidan yari da rage kalaman kiyayya. Abin jira a gani shi ne ko bangarorin za su cika wadannan alkawura.
Ambasada Thomas-Greenfield ta ce “Lokaci ya yi da bangarorin za su ajiye makamansu su dawo da mulkin farar hula.” Za mu yi dukkan mai yuwuwa don taimakawa al’ummar Sudan wajen tabbatar da ‘yanci, zaman lafiya da adalci da suke bukata.”