Anncr: Yanzu kuma sai Sharhin Muryar Amurka; mai bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka:
Anncr: Yanzu kuma sai sharhin Muryar Amurka mai bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka.
"Afrika ta fi karfin ‘yan waje da ke ƙoƙarin mallake nahiyar. Kuma Afirka ta fi karfin masu mulkin kama karya da ke siyar da bindigogi masu arha, tura sojojin haya kamar kungiyar Wagner, ko hana hatsi ga masu fama da yunwa a duniya."
Kawar da yunwa na ɗaya daga cikin manyan manufofin Hukumar Raya Ƙasashe masu tasowa ta Amurka, USAID.
"Za mu ci gaba da kawar da wadanda ke neman yin amfani da tsarin hadahadar kudade na Amurka da na kasa da kasa don samar da kudade da kuma shiga ayyukan ta'addanci."
“A yanzu Shugaba Biden ya kaddamar da wani shiri mai suna Shirin Shugaban Kasa na Gaggawa don rungumar sauyi, kuma ya yi alkawari cewa za mu taimakawa akalla rabin biliyan mutane a kasashe masu tasowa, musamman a Afirka"
A matsayinta na mamba a yarjejeniyar da aka cimma a Geneva, akwai nauyi da ya rataya a wuyan Rasha na kada ta kai hari kan muhimman kayayyaki da suke da “hadari, ciki har da madatsar ruwa” musamman idan wannan hari zai haifar da illa ga fararen hula.
Ya zuwa lokacin da suka kammala samamen, akalla mutum 500 ne suka mutu. Akwai rahotanni da ke cewa an azabtar da mutane tare an ci zarafin mata akalla 58, ciki har da wadanda aka yi wa fyade.
Yayin da wasu sassan Afirka da Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da fuskantar matsalar karancin abincin da ba a taba ganin ba irin ta ba, Rasha ta dakile ayyukan noma a Ukraine tare da hana aikawa da kayan abinci zuwa sassan duniya ta tekun Bahr Al Aswad.
Shirin ATA, shiri ne da alhakin nasararsa ya rataya a wuyan sashen yaki da ta’addanci da ayyukan diflomasiyya na ma’aikatar tsaron Amurka.
Load more